Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya amince da sake nada Aliyu Aziz a matsayin shugaban Hukumar Kula da tsarin shaidar zama dan kasa karo na biyu.
Babban manajan hukumar na sashen ayyuka da yada labarai Abdullahi Umar ya sanar da haka, a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Abuja.
Abdullahi Umar, ya ce sakon sabunta wa’addin mulkin Aziz ya na kunshe ne a cikin wata wasika da sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ya aike da ita.
A
cewar sa, wa’addin Aliyu Aziz na biyu zai fara aiki ne a ranar Juma’a 22 ga
watan Nuwamba.














































