Home Labaru Takaddama: An Gargadi ‘Yan Siyasa Kan Batun Jamal Kashoggi

Takaddama: An Gargadi ‘Yan Siyasa Kan Batun Jamal Kashoggi

438
0

Dangantaka tsakanin kasashen Saudiyya da kuma Turkiyya ta yi tsami tun bayan kisan gillar da aka yiwa ‘dan jaridar a ofishinn jakadancin Saudiyya dake birnin Santanbul lamarin da ya janyowa Yarima Mohammaed bn Salman suka daga bangarori daban-daban.
Yariman dai ya bukaci duk wanda yake da gamsasshiyar shaida kan kisan Jamal Kashoggi da ya taimaka ya sanar da kotun Saudiyya don a yiwa iyalan mamacin adalci.
A baya dai hukumar CIA ta bayana cewar akwai yiwuwar yariman na Saudiyya Mohammed Bn Salman ne ya bada umarnin kisan kan duk kuwa da cewar tuni masu gabatar da kara a Saudiyya suka wanke shi bayan tsare mutane da dama a matsayin masu da hannu a kisan dan jaridar.

Leave a Reply