Home Labaru Ta’addanci: Mutane 8 Sun Mutu A Hare-Hare A Somaliya

Ta’addanci: Mutane 8 Sun Mutu A Hare-Hare A Somaliya

414
0

Wasu tagwayen hare-haren kunar bakin wake sun kashe mutane da dama a kasar Somaliya.
Mayakan al-Shabaab sun dauki alhakin harin kunar bakin wake da ya kashe mutane akalla 8 tare da jikkata wasu da dama a kusa da ginin majalisar dokokin kasar a wannan Asabar.
Wadanda suka shaidar da harin na cewa bam din ya rusa shaguna da gidajen mutane da dama. Rahotanni sun ce an kuma samun tashin wani bam a babban titin zuwa filin jirgin sama da ke babban birnin kasar Mogadishu, Sai dai babu rahotannin asarar rayuka a harin na biyu.
‘Yan sanda sun killace dukkannin titunan da suka hade da wurin da aka kai hare-haren, jami’an agajin gaggawa kuma na ci gaba da ayyukan ceto. Tun dai ba yau ba mayakan al-Shabaab da ke ikirarin zama reshen kungiyar al-Qa’ida na zama barazana ga rayuwar fararen hula tun bayan da kungiyar ta lashi takobin ganin bayan gwamnati.

Leave a Reply