Home Labaru Magudin Zabe: Na’urar Card Reader Ce Ta Taimaka Min Na Lashe Zaben...

Magudin Zabe: Na’urar Card Reader Ce Ta Taimaka Min Na Lashe Zaben 2015 – Buhari

1002
0
Kada Ku Tausayawa ‘Yan Bindiga- Buhari
Kada Ku Tausayawa ‘Yan Bindiga- Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bayyana yadda na’urar tantance masu kada kuri’a wato ‘Card Reader’, ta taka gagarumar rawa wajen taimaka masa samun nasarar lashe zaben shekara ta 2015.

A wata hirar musamman da ya yi da manema labarai, shugaba Buhari ya ce abu ne mai wuya wadanda ba su cikin gwamnati su lashe zabe, saboda yadda shugabannin da ke karagar mulki ke gudanar da magudi domin ba wadanda su ke so damar hawa karagar mulki wajen rubuta alkaluman karya.

Shugaba Buhari, ya ce amfani da na’urar tantance masu kada kuri’a ya taimaka wajen ba jama’a damar zaben abin da su ke so, da kuma tabbatar da ganin an kauce wa yin magudi.

Buhari ya bayyana cewa, zai maida hankali wajen kirkiro ayyukan yi ga matasa tare da samar da wutar lantarki da tabbatar da tsaro da kuma yaki da cin hanci da rashawa a wa’adin mulkin san a biyu.

Ya ce gwamnatin sa za ta maida hankali wajen sake manhajar ilimin kasa baki daya, wanda zai karkata zuwa bangaren kimiyya da fasaha, yayin da za su cigaba da tallafa wa marasa karfi da kudade tare da kananan ‘yan kasuwa da matasa da kuma mata.