Jam’iyyar PDP, ta ce zargin da Fadar Shugaban kasa ta yi cewa wasu fitattun ‘yan Nijeriya na shirin yi wa Shugaban kasa, bita da kulli ya nuna cewa gwamnatin jam’iyyar APC ta gaza kenan.
Fadar Shugaban kasa dai ta ce wasu manyan ‘yan siyasar da ba a bayyana sunayen su ba, su na yi wa shugaba Buhari, da manofofin sa zagon-kasa.
A cikin wata sanarwa da mai Magana da yawun jam’iyyar PDPn Kola Ologbondiyan ya fitar, PDP ta ce a bayyane ya ke gwamnatin APC ta na fama da gazawa ta kowane bangare a harkokin mulki.
Jam’iyyar PDP, ta shawarci fadar shugaban kasa ta daina yawo da hankalin ‘yan Najeriya, ta kuma daina zargin manyan mutane a kan gazawar gwamnatin APC.
You must log in to post a comment.