Home Labaru Kiwon Lafiya Annobar Korona: Mutum 21 Sun Mutu A Najeriya A Ranar Litinin

Annobar Korona: Mutum 21 Sun Mutu A Najeriya A Ranar Litinin

156
0

Hukumar daƙile yaɗuwar cutuka a Najeriya, NCDC, ta ce mutum 21 ne suka mutu sakamakon cutar korona ranar Litinin a Najeriya, kazalika, ƙarin mutum 676 sun kamu da cutar a ranar.

Bayanan sun nuna cewa an samu sabbin wadanda suka kamu da annobar ce a jihohi 19 da suka haɗa da jihar Legas da aka samu mutum 227, sai Rivers mutum 73, Neja mutum 69, Filato 56, Abuja 50, Kano 44, sai kuma Oyo  mai mutum 43.

Sauran sun hada da Ogun da aka samu mutum 27, Gombe 18, Ondo 15, Enugu da Osun 10-10, Cross River da Edo 8-8, Nasarawa 7, Bauchi 4, da Kaduna 3, Ekiti 2 da Zamfara 2-2.

Hukumar ta ce ya zuwa yanzu, jumillar mutum dubu 131 da 918 ne suka harbu da cutar a Najeriya, yayin da mutum dubu 1 da 607 suka mutu, sai kuma mutum 106 da 275 da aka sallama bayan sun warke.