Hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa INEC, ta sanar da ranar da za a fafata tsakanin Sanata Dino Melaye da Sanata Smart Adeyemi a zaben kujerar dan majalisar dattawa na mazabar Kogi ta yamma.
Kwamishanonin hukumar sun bayyana Asabar, 30 ga watan Nuwamba na shekara ta 2019 a matsayin ranar da za a karasa zaben.
Jami’in yada labarai na hukumar Festus Okoye, ya ce hukumar zabe ta ta zabi ranar Asabar, 30 ga Nuwamba, 2019 domin karasa zaben mazabar Kogi ta yamma.
A
ranar Asabar, 16 ga wata ne, hukumar zabe ta ce ba a samu wanda ya yi nasara a
zaben kujerar dan Majalisar dattawa na mazabar Kogi ta yamma a zaben da ya
gabata ba.