Home Labaru Kiwon Lafiya Samun Kariya: Wasu Daliban Najeriya Sun Kera Mutum-Mutumin Da Ke Hana Ma’aikatan...

Samun Kariya: Wasu Daliban Najeriya Sun Kera Mutum-Mutumin Da Ke Hana Ma’aikatan Lafiya Kamuwa Da Cutar Korona

122
0

Wasu daliban makarantar sakandiri a Najeriya sun kirkiro wani mutum-mutumi mai suna Mairobot bisa la’akari da yadda jami’an lafiya a Najeriya suka rinka kamuwa da cutar korona har ta kai su ga mutuwa, a zagayen annobar na farko.

A dai dai wannan lokaci da duniya ke shaida dawowar annobar a karo na biyu, daliban sun ce sun kirkiro wannan mutum-mutumi ne domin takaita kamuwar jami’an na lafiya daga cutar mai kisa.

Wannan fasaha ta mutum-mutumi an yi ta ne da siffar wani akwakwu mai taya ta yadda zai yi zarya tsakanin marasa lafiya.

Mairobot na da kafa hudu sannan na amfani da na’urar daukar hoto a matsayin idanu da kuma na’urar aike sako ta Infrared wajen gwada zafin jikin marasa lafiya.

Ita wannan fasaha ta Mairobot na da matuki wanda shi ne idanun ta.