Home Labaru Ta’addanci: Yaro Ya Daba Wa Mahaifin Sa Wuka Har Lahira A Jihar...

Ta’addanci: Yaro Ya Daba Wa Mahaifin Sa Wuka Har Lahira A Jihar Kano

805
0

Wani matashi mai suna Habibu Ibrahim, ya kashe mahaifin sa Malam Ibrahim Salihu mai shekaru 80 da wuka har lahira a kauyen Asada na karamar hukumar Doguwa a jihar Kano.

Kakakin hukumar ‘yan sanda na jihar Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce daya daga cikin ‘yanuwan Habibu mai suna Yahaya Ibrahim, ya kai kara ofishin su da ke Doguwa cewa kanin sa ya caka wa mahaifin su wuka cikin dare.

Ya ce, yayin da su ka samu labarin, jami’an ‘yan sanda sun garzaya da shi asibitin Doguwa domin jinya, amma ya mutu da misalin karfe 6:30 na asuba.

DSP Abdullahi, ya ce bayan gudanar da binciken da ya kamata a kan gawar, an mika ta ga iyalan domin jana’izar sa bisa tsarin addinin Musulunci.

Ya ce binciken da su ka gudanar ya nuna cewa, yaron dan kwaya ne kuma ya aikata lamarin ne bayan ya bugu da kayan maye, sun kuma samu nasarar kama shi ne bayan ya tsere.