Home Labaru Ta’addanci: ’Yan Sanda A Benue Sun Ce Mutane 4 Suka Mutu

Ta’addanci: ’Yan Sanda A Benue Sun Ce Mutane 4 Suka Mutu

174
0
’Yan Sanda
’Yan Sanda

Rundunar ‘yan sanda jihar Benue ta bada tabbacin kisan mutum hudu wadanda suka halarci jana’iza a shiyyar Tongov dake karamar hukumar Katsina Ala.

Karanta Wannan: Yaki Da Ta’addanci: Rundunar Soji Ta Sha Alwashin Magance Matsalar Tsaro

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mukaddas Garba ne ya sanar da kamfanin dillacin labaran Najeriya cewar lamarin ya auku ne a wurin jana’izar Tor.

Kwamishinan, ya ce tu ni hukumar ‘yan sanda ta fara bincike a kan lamarin, inda ya bada tabbacin cewa za a kama masu laifin nan bada jimawa ba.

Ya roki al’ummar yankin cewa duk wanda yake da wani bayani da zai taimakawa ‘yan sanda wurin binciken ya yi gaugawar sanar da hukuma.

Wani ganau akan lamarin, ya ce  mutane sama goma ne suka budawa masu zaman makoki wuta da bindigogi, inda suka kashe mutane da dama a yayinda wasu suka sami rauni.