Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya tsohon shugaban kasa a lokacin mulkin Soji, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, murnar cika shekara 78 da haihuwa.
Karanta Wannan: Karbo Kudade: Gwamnatin Tarayya Na Kokarin Kalubalantar Hukuncin Kotun Burtaniya
Mai magana da yawun shugaban kasa Garba Shehu, ya ce a madadin gwamnatin tarayya da Iyalinsa da sauran ‘yan Najeriya Shugaban kasa Buhari na taya Ibrahim Badamasi Babangida murna.
Shugaban kasa ya jinjinawa irin kokarin da tsohon shugaban kasa ya yi wa Najeriya a rayuwar sa, na namijin kokari da bautar da ka yi a gidan Soja domin tsare martabar Najeriya. .
Buhari ya kara da cewa gwamnati
na godiya da irin kishin kasa da ya nuna wajen sha’anin tafiyar da Najeriya, inda ya yi
addu’a ga Ubangiji ya kara masa lafiya da kwarin gwiwa domin taimakawa najeriya.
You must log in to post a comment.