Home Labaru Martani: Ohanaeze Tayi Allah-Wadai Da Cin Zarafin Sanata Ekweramadu A Jamus

Martani: Ohanaeze Tayi Allah-Wadai Da Cin Zarafin Sanata Ekweramadu A Jamus

166
0

Kungiyar Ohanaeze Ndigbo dake kare muradun kabilar Igbo, ta yi Ala-Wadai da yunkurin cin zarafin tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa Ike Ekweremadu, da wasu masu goyon bayan kafa kasar Biafra suka yi.

Lamarin dai ya auku ne a kasar Jamus, yayin da Sanata Ekweremadu ke halartar wani taron al’adu a birnin Nurnberg, da kabilar Igbo ke shiryawa a duk shekara a Jamus.

Karanta Wannan: Tsaro: Rundunar Soji Ta Bukaci Mutanen Yankin Kudu Maso Gabas Kada Su Razana Da Yawaitar Jami’anta

Ekweremadu, ya ce jim kadan bayan fara taron ne, wasu da suka bayyana kansu a matsayin ‘ya’yan haramtacciyar kungiyar IPOB suka bayyana, tare da shan alwashin taron bai zai ci gaba da gudana ba, saboda yadda ake cin zarafin ‘yan uwansu a gida Najeriya.

Dangane da haka ne Ekewremadu ya yi kokarin lallashin su, amma suka far masa da jifa, abinda yasa aka gaggauta dauke shi daga wurin.