Home Labaru Sake Fasalta Najeriya: El-Rufa’i Ya Goyi Baya

Sake Fasalta Najeriya: El-Rufa’i Ya Goyi Baya

101
0

Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El Rufai ya bayyana goyan bayan
sa ga masu bukatar sake fasalin Najeriya da zimmar sake gina ta, amma
kuma ya bukaci a bi hanyar dimokiradiya domin cimma biyan bukata.

A sakon da ya aike wa manema labarai ta hannun mai Magana da yawun
sa Muyiwa Adekeye, El Rufai, ya bayyana sake fasalin Najeriyar a
matsayin hanyar da za ta inganta sha’anin mulki da rage dogaro da
gwamnatin tarayya da daidaita yanayin rarraba matakan iko da kuma
aiwatar da su.

Gwamnan, ya ce akwai dama ta musamman ga daukacin ‘yan Najeriya
da suka amince da wannan tsari wajen aiki tare domin ganin an cimma
nasara, sai dai ya ce tsarin da zai sake fasalin tafiyar da Najeriya zai
samu ne kawai ta hanyar bin matakan da kundin tsarin mulki ya tanada,
wanda ya ba majalisar dokoki damar aiwatar da shi.

El Rufai ya ce masu bukatar sauyin na iya amfani da wakilan su da ke
Majalisa wajen gabatar musu da bukatar domin amincewa da ita, kafin a
mika wa Majalisun Jihohin su kuma a samu kashi biyu bisa 3 da za su
goyi baya, kafin shugaban kasa ya sanya hannu.

Ya ce babu wata hanya ta daban da za a bi wajen sake fasalin Najeriya
da ta wuce wannan, kuma za a samu nasarar ce kawai wajen janyo
hankalin juna da fadakarwa tare da hadin kai amma ba barazana ba.