Home Labaru Ta’addanci: ‘Yan Bindiga Sun Sace Uwa Da ‘Yar Ta A Jihar Adamawa

Ta’addanci: ‘Yan Bindiga Sun Sace Uwa Da ‘Yar Ta A Jihar Adamawa

5
0
Wasu 'yan bindiga sun kai wa ofishin ‘yan sanda hari a Yola babban birnin Jihar Adamawa sannan suka sace wata mata da ‘yar ta.

Wasu ‘yan bindiga sun kai wa ofishin ‘yan sanda hari a Yola babban birnin Jihar Adamawa sannan suka sace wata mata da ‘yar ta.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Sulaiman Nguroje, ne ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a ranar Lahadi.

A cewar sa, maharan sun far wa ofishin ne da misalin ƙarfe 2 na daren Lahadi amma babu wanda ya ji rauni ko kuma kisa.

Ya ce maharan sun kai wa gidan wani Alhaji Umaru ne da ke Nasarawa B, a Ƙaramar Hukumar Yola ta Kudu harin inda suka rabu gida biyu domin su ɗauke hankalin ‘yan sanda.

Ya ce yayin da wasu ke kai wa gidan Alhaji Umaru hari suka ɗauki matar sa da ‘yar sa, sai wasu suka kai wa ofishin ‘yan sanda hari.

Ya ƙara da cewa Kwamashinan ‘yan Sandan jihar Mohammed Barde ya bayar da umarnin tura dakaru ciki har da na kwantar da tarzoma zuwa yankin na Nguroje don bin sahun maharan.