Home Labaru Sare Itatuwa: Masani Ya Ce Najeriya Na Dab Da Fuskantar Matsalar Muhalli

Sare Itatuwa: Masani Ya Ce Najeriya Na Dab Da Fuskantar Matsalar Muhalli

5
0
Wani kwararre a kan harkar muhalli, Azibaola Robert, ya koka kan yadda ake yawan sare bishiyoyi a Najeriya, inda ya ce hakan na babbar barazana ce ga iskar da mutane da dabbobi ke shaka.

Wani kwararre a kan harkar muhalli, Azibaola Robert, ya koka kan yadda ake yawan sare bishiyoyi a Najeriya, inda ya ce hakan na babbar barazana ce ga iskar da mutane da dabbobi ke shaka.

Masanin ya bayyana hakan ne ranar Asabar lokacin da yake jawabi ga manema labarai yayin wani taron yini 14 na nuna wani faifan bidiyo kan muhalli da ke gudana a garin Otakeme na Karamar Hukumar Ogbia ta Jihar Bayelsa.

A cewar sa, muddin ba a yi wa tufkar saran itatuwa barkatai hanci ba, akwai yuwuwar Najeriya ta fuskanci matsalar da ta shafi muhalli nan ba da jimawa ba.

Mista Azibaola ya ce abin takaici ne yadda saran bishiyoyi ba tare da ana dasa wasu ba yake barazana ga manyan dazukan da ke yankin Neja Delta, wanda ya ce tuni ma ya fara shafar muhalli.