Babban basaraken Jihar Taraba, Aku Uka na Wukari, Dokta Shekarau Agyo ya mutu.
Marigayin, wanda shi ne ‘Sarkin Jukunawa’ ya mutu ne yana da shekara 84 a duniya.
Wakilin Aminiya ya jiwo cewa Sarkin mai daraja ta daya kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Taraba ya mutu ne ranar Asabar a fadar sa dake Wukari bayan yayi fama da rashin lafiya.
Dokta Shekarau Agyo, dai ya dare kan karagar mulki ne a watan Agusta na shekarar1976, ya shafe kimanin shekara 45 kenan a kan gadon mulki.
Wata majiya daga gwamnatin Jihar ta shaida wa Aminiya cewa a al’adance, Gwamnan Jihar ne kawai zai iya bayar da sanarwar mutuwar Sarkin a hukumance bayan an kammala wasu al’adu kamar yadda yake kunshe a al’adun ’yan kabilar ta Jukun.