Home Labaru Ta’addanci: ‘Yan Bindiga Sun Sace Mutane 15 A Wata Mujami’a A Jihar...

Ta’addanci: ‘Yan Bindiga Sun Sace Mutane 15 A Wata Mujami’a A Jihar Kaduna

290
0

Rahotanni na cewa, wasu ‘yan bindiga sun kai hari a wata mujami’a da ke kauyen Dankade a karamar hukumar Igabi, inda su ka sace mutane 15 ciki kuwa su har da limamin cocin.

Shugaban cocin Rebaran Nathan Waziri, ya ce wadanda aka sace sun hada da limamin cocin Rev Zachariya Ido da ‘yar sa da wasu mutane 13.

Kakakin rundunar ‘yan Sanda na jihar kaduna Jihar Yakubu Sabo ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce jami’an su su na farautar wadanda su ka sace mutanen, wadanda su ka hada da maza 5 da mata 10. Harin dai ya zo ne kwana daya bayan kofar ragon da matasa su ka yi wa wasu masu garkuwa da mutane a unguwar Kawo da ke Kaduna su ka hallaka daya daga cikin su.