Home Labaru Kiwon Lafiya Kiwon Lafiya: Kungiyar Likitoci Ta Koka Da Karancin Likitoci A Jihar...

Kiwon Lafiya: Kungiyar Likitoci Ta Koka Da Karancin Likitoci A Jihar Legas

277
0

Kungiyar likitoci ta ‘Medical Guild’ reshen jihar Legas, ta bukaci gwamnatin jihar ta kara yawan ma’aikata a asibitocin da ke fadin jihar domin inganta kiwon lafiyar al’ummomin ta.

Shugaban Kungiyar Babajide Saheed, ya ce rashin yin haka zai iya gurgunta ayyukan fannin kiwon lafiyar jihar, ganin cewa tun farko ana fama da wasu matsaloli.

Ya ce yanzu haka likita daya a asibiti ya na aikin likitoci biyu ne ko kuma uku, sannan albashin sa ba wani abin a zo a gani ba ne.

Wasu kwararrun ma’aikatan kiwon lafiya ai sun koka a kan yawan mutuwar kananan yara da mata da ake ake fama da shi a fadin Nijeriya.