Home Labaru Tsaro Tsaro: ‘Yan Sanda Sun Sake Kama Masu Garkuwa Da Mutane Sama Da...

Tsaro: ‘Yan Sanda Sun Sake Kama Masu Garkuwa Da Mutane Sama Da 70

356
0

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta bayyana nasarar sake kama masu satar mutane da yin garkuwa da su sama 70 da su ka addabi jama’a a sassan jihar Katsina da makwaftan ta.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar ta Katsina Sanusi Buba, ya ce sun kwace tarin makamai da su ka kunshi, bindigogi kirar AK 47 guda 43, da bindigogi kirar gida guda 19, da kuma manya bindigogi masu sarrafa kan su guda 2 da wasu kananan bindigogi biyu.

‘Yan sandan, sun kuma kwace harsasai sama dubu 1 da 500, da Babura 44 da motoci 5, sai kuma kayayyakin abinci da wasu karin kayan da ‘yan bindigar ke amfani da su.Daga cikin wadanda aka kama, akwai ‘yan bindigar da su ka sace surukar gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari mai suna Hauwa Yusuf ‘yar shekaru 80.

Leave a Reply