Home Labaru Ta’addanci: ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Da Dama A Kauyen Rafin Kada...

Ta’addanci: ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Da Dama A Kauyen Rafin Kada Na Jihar Taraba

1233
0

Rahotanni na cewa, wasu ‘yan bindiga sun kai hari garin Rafin Kada da ke hanyar Takum zuwa Wukari a jihar Taraba, inda su ka kashe mutane da dama.

Wata majiya ta ce ‘yan bindigar sun shiga garin ne daga jihar Benue, inda su ka kone gidaje da dama sannan su ka kashe mutane da dama.

Haka kuma, ‘yan bindigar sun kai wa motar shugaban karamar hukumar Wukari hari da wata mota dauke da sojoji a hanyar su ta zuwa garin Rafin Kada, domin amsa kiran neman dauki da aka yi masu.

Majiyar ta ce, ‘yan bindigar sun yi wa wasu matasan garin kwanton-Bauna su ka kashe biyu daga cikin su, yayin da suka yi yunkurin bin sahun ‘yan bindigar domin daukar fansa.

Rafin Kada dai shi ne garin ‘yan kabilar Jukun na uku da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne su ka kaiwa hari tare da kashe mutane a cikin mako daya. Shugaban karamar hukumar Wukari Mr Adi Daniel ya shaida wa manema labarai cewa, ‘yan bindiga masu yawa sun kai hari a Rafin dadi a safiyar Talatar da ta gabata, inda su ka kashe wasu mutane tare da kone gidaje 32.