Home Labaru Daukar Aiki: Kungiyar Dalibai Ta Kasa Ta Yi Fatali Da Sharuddan Kamfanin...

Daukar Aiki: Kungiyar Dalibai Ta Kasa Ta Yi Fatali Da Sharuddan Kamfanin NNPC

316
0

Kungiyar Daliban Jami’o’i ta Kasa NANS, ta yi fatali, tare da yin Allah-wadai da tsarin da kamfanin Man Fetur na NNPC ya bi wajen daukar sabbin ma’aikata.

Ta ce abin da kamfanin NNPC ya nema daga ka’idojin da tilas wanda ke menan aikin zai cike, ba a tsara su domin a dauki masu karamin karfi da kuma ‘ya’yan talakawa ba.

Jami’in Yada Labarai na kungiyar Adeyemi Azeez ne ya fitar da sanarwar kin amincewa da matakan da kamfanin NNPC ya dauka.

Kungiyar ta ce, da gangan aka gindaya sharuddan domin kawai a ture wadanda su ka cika takardun neman aiki a kamfanin, musamman ‘ya’yan marasa galihu.

Adeyemi Azeez, ya ce ba a banza yawan yajin aiki ya gurgunta harkokin ilmi a Nijeriya ba, shi ya sa dalibin da zai yi kwas na shekaru hudu, sai ya kare da zama har na tsawon shekaru 9 zuwa goma kafin ya kammala. Don haka kungiyar ta ce ba za ta yarda da wannan kullalliya da kamfanin NNPC ya shirya domin hana wadanda su ka cancanta da dama samun aikin ba.