Home Labaru Ta’addanci: ‘Yan Bindiga Sun Kai Wa Tawagar Sarkin Kauran Namoda Hari

Ta’addanci: ‘Yan Bindiga Sun Kai Wa Tawagar Sarkin Kauran Namoda Hari

253
0

Rahotanni daga jihar Zamfara na cewa, ‘yan bindiga sun tare
tawagar Sarkin Kauran Namoda Manjo Sanusi Muhammad
Asha, inda su ka kashe mutane takwas ciki har da jami’an ‘yan
sanda uku.

Majiyoyi sun ce, sarkin ya na kan hanyar sa ne zuwa wani taro a
Gusau, yayin da ‘yan bindigar su ka afka wa tawagar sa su ka
kashe ‘yan sanda uku.

Daga cikin wadanda aka kashe a tawagar akwai wani direba da
babban dogarin sarki da wani Dan Amal, wanda kawu ne ga
sarkin Kauran Namoda.

Zamfara dai ta na daga cikin jihohin Arewa da ke fuskantar
kallubalen tsaro, inda ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane
ke yawan kai wa jama’a hari akai-akai.