Home Labaru Hangen Nesa: Obasanjo Ya Lissafa Matsaloli Uku Da Ke Addabar Nijeriya

Hangen Nesa: Obasanjo Ya Lissafa Matsaloli Uku Da Ke Addabar Nijeriya

122
0

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya ce akwai bukatar
karfafa alaka tsakanin gwamnati da al’umma wajen shawo kan
matsalolin Nijeriya.

Obasanjo ya bayyana haka ne, yayin da ya kai ziyarar ta’aziyya
ga gwamnan jihar Oyo Seyi Makinde, bisa rasuwar mahaifiyar
sa Abigail, inda ya ce ta tabbata cewa gwamnati ba za ta iya ita
kadai ba.

Tsohon shugaban kasar, ya bayyana rashin tsaro da rashin
daidaituwar tattalin arziki, da rashin shugabanci nagari a
matsayin manyan kalubale, don haka ya shawarci al’umma su
dage wajen kawar da wadannan matsaloli.

Da ya ke tsokaci a kan batun cire manyan hafsoshin tsaro a
kokarin magance matsalar tsaro, Obasanjo ya ce ya na da
shawarar da zai ba su a matsayin uba, amma ba zai fada duniya
ta ji ba.