Home Labaru Ta’Addanci: Sabon Kwamishinan ‘Yan Sanda Na Jihar Zamfara Ya Gargadi ‘Yan Bindiga

Ta’Addanci: Sabon Kwamishinan ‘Yan Sanda Na Jihar Zamfara Ya Gargadi ‘Yan Bindiga

59
0
Zamfara New Police Head

Sabon kwamishinan ‘yan sanda na jihar Zamfara Yakubu Elkana, ya ja kunnen ‘yan bindigar da su ka addabi jihar cewa su zubar da makamai ko kuma su fuskanci hukunci mai tsanani.

Elkana ya bayyana haka ne yayin tattaunawa da manema labarai a Gusau, inda ya hori ‘yan bindiga su yi gaugawar ba gwamnatin jihar hadin kai wajen samar da zaman lafiya ko su ga aiki da cikawa.

Kwamishinan ya kara da rokon jama’ar gari su yi kokarin ba ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro hadin kai, domin dakatar da duk wasu ayyukan ta’addanci a fadin jihar Zamfara.

Haka kuma, kwamishinan ya yaba wa ‘yan jarida bisa yadda su ke ba ‘ya sanda hadin kai domin tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Elkana, ya ce ‘yan jarida su na kokari kwarai kuma mutanen kirki ne, don haka ya mika godiya a gare su bisa hadin kan da su ke ba ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro.