Home Labaru Kasuwanci Rance: Nijeriya Ta Ci Bashin N15.51Tn A Hannun Cbn Sabanin N33.11Tn Da...

Rance: Nijeriya Ta Ci Bashin N15.51Tn A Hannun Cbn Sabanin N33.11Tn Da Ake Bin Ta

54
0
Buhari-CBN

Jimmillar kudin da gwamnatin tarayya ta karba bashi daga hannun babban bankin Nijeriya ya kai Naira Tiriliyan 15 da Biliyan 51, sabanin Naira Biliyan 640 kafin hawa mulkin shugaba Buhari, kamar yadda wasu bayanai daga bankin CBN su ka nuna.

Ofishin kula da basussuka ya ce, wannan bashin dai, daban ne da bashin Naira Tiriliyan 33 da biliyan 11 da ake bin Nijeriya a bankunan cikin gida da na kasashen waje.

Gwamnati dai ta kan karbi bashi daga hannun bankin CBN domin tafiyar da harkokin ta idan aka samu matsala da kasafin kudi na shekara.

A Sashe na 38 na dokar bankin CBN ta shekara ta 2007, bankin na iya ba gwamnatin tarayya bashi idan aka samu matsala da kasafin kudi, kuma bankin na iya kara kudin ruwa.

Tsakanin watannin Junairu da Yuni na shekara shekara ta 2021 dai, gwamnatin tarayya ta karbi bashin Naira Tiriliyan 2 da Biliyan 400 daga babban bankin Nijeriya CBN.