Home Labaru Ashura: Mabiya Shi’A Za Su Gudanar Da Muzahara A Garin Kaduna

Ashura: Mabiya Shi’A Za Su Gudanar Da Muzahara A Garin Kaduna

51
0

Mabiya akidar shi’a sun sanar da shirin gudanar da muzahara a ranar 19 ga watan Agusta na shekara ta 2021 a garin Kaduna.

Daya daga cikin jagororin kungiyar malam Aliyu Umar, ya ce muzaharar za ta gudana cikin lumana da kwanciyar hankali kamar yadda su ka saba yi duk shekara.

Da ya ke zanatawa da manema labarai a Kaduna, malam Aliyu ya ja hankalin al’umma da cewa, su mutane ne masu son zama lafiya, don haka a daina kallon su a matsayin mutane masu tada son kayar baya.

Ya ce tuni mutanen su sun shirya gudanar da muzahar lami lafiya cikin kwanciyar hankali, tare da alkawarin ba jami’an tsaro hadin kai domin tabbatar da tattakin ya gudana ba tare da samun wata matsala ba.