Home Labaru Ibtila’i: Ambaliyar Ruwa Sama Ta Rushe Gidaje 48 Ta Raba Mutane 285...

Ibtila’i: Ambaliyar Ruwa Sama Ta Rushe Gidaje 48 Ta Raba Mutane 285 Da Gidajen Su A Filato

280
0

Wata mummunar ambaliyar ruwa a jihar Filato, ta rushe gidaje a kalla 48 tare da raba a kalla mutane 285 da gidajen su a karamar hukumar Mangu.

Lamarin, wanda ya faru da yammacin ranar Talatar da ta gabata, ya jefa gwamantin jihar Filato da karamar hukumar Mangu a cikin damuwa.

Ambaliyar ta yi sanadiyyar rushewar gidaje gaba daya, ko kuma yin awon gaba da rufin gidajen, lamarin da ya tilasata jama’a barin yankunan da abin ya shafa.

Tuni dai mataimakin gwamnan jihar Farfesa Sonni Tyoden tare da wakilan hukumar bada agajin gaugawa na jihar su ka ziyarci karamar hukumar Mangu, inda su ka jajenta wa jama’a tare da daukar alkawarin ba su tallafi.

Mataimakin gwamnan, ya yi kira ga jama’ar yankin Toghomwol-Bungha su dauki abin da ya faru a matsayin kaddara daga Ubangiji, inda a karshe ya ba wadanda ibtila’in ya shafa tallafin Naira miliyan daya daga aljihunsa.