Home Home Ta’addanci: Kwamishinan Filaye Na Jihar Enugu Ya Tsallake Rijiya Da Baya

Ta’addanci: Kwamishinan Filaye Na Jihar Enugu Ya Tsallake Rijiya Da Baya

96
0
Kwamishinan filaye na jihar Enugu Chidi Aroh ya tsallake rijiya da baya, bayan wasu ‘yan bindiga sun kai ma shi hari yayin da ya ke komawa daga jihar Anambra inda ya halarci wani taro.

Kwamishinan filaye na jihar Enugu Chidi Aroh ya tsallake rijiya da baya, bayan wasu ‘yan bindiga sun kai ma shi hari  yayin da ya ke komawa daga jihar Anambra inda ya halarci wani taro.

Biyu daga cikin jami’an tsaron sa da su ka yi artabu da ‘yan bindigar ana fargabar sun mutu, domin har yanzu ba a gano gawarwakin su ba.

Wata Majiyar ‘yan sanda ta ce, an kashe jami’an tsaron kwamishinan biyu ne a lokacin da ‘yan bindigar su ka yi wa kwamishinan kwanton-bauna.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Anambra Ikenga Tochukwu ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce lamarin ya faru ne a kan hanyar Ukpo zuwa Nimo.

Ya ce bayan samun rahoton, rundunar ta tura jami’an ta zuwa yankin, amma har yanzu ba a san inda ‘yan sandan biyu su ke ba.