
Wata babbar kotun tarayya da ke zama a birnin Jos na jihar Filato, ta yanke wa tsohuwar ministar albarkatun ruwa Sarah Ochekpe hukuncin daurin watanni uku a gidan yari.
Kotun ta kuma yanke wa tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na jihar Raymond Dabo da Evangelist Leo Sunday Jitung hukuncin daurin watanni uku kowannen su a gidan kaso.
Mai shari’a Musa Kurna ya zartar da hukuncin, bayan dukkan mutanen uku sun shafe tsawon shekaru hudu su na fuskantar shari’a bisa zargin hada kai da kuma wawure kudaden al’umma.













































