Home Labaru Zaben 2019: Kungiyar Kare Hakkin Bil’adama Ta Ce Buhari Ya Yi Nasara...

Zaben 2019: Kungiyar Kare Hakkin Bil’adama Ta Ce Buhari Ya Yi Nasara Cikin Yanayi Mai Tsanani

356
0

Kungiyar Kare Hakki Bil-Adama Ta Human Rights Watchta Ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Ya Yi Nasarar Lashe Zaben A Ranar 23 Ga Watan Fabrairu Cikin Tsanani Da Rikicin Zabe.

A Wani Rahotoda Kungiyar Ta Fitar Wanda Ta Wallafaa Ranar Litinin Nin Din Da Ta Gabata, Kungiyar Ta Zargi Hukumomin Tsaron‘Yan Sanda Da Soji A Kan Yadda Su Ka Bada Gudunmuwa Wajen Tada Tarzoma A Lokacin Zabe.

Kungiyar Ta Kuma Ce,Abubuwa Mara Dadi Sun Faru A Lokacin Zaben , Wanda Suka Hada Da Af’kuwar Hare-Haren Kungiyar Boko Haram A Yankin Arewa Maso Gabas Da Rikicin Makiyaya Da Manoma A Yankin Kudanci Da Kuma Arewa Ta Tsakiya Da Kuma Ta’adin Masu Garkuwa Da Mutane A Jihohin Zamfara Da Katsina Da Kuma Kaduna.

Wakiliyar Kungiyar A Nijeriya, Anietie Ewang Ta Ce Babu Wani Ci Gaban Tsaro Da Aka Samu A Lokacin Zaben A 2019 Idan An Kwatanta Da Zabukan Da Suka Ganbata A Tarihin Nijeriya.

A Karshe Ewang Ta Bukaci Shugaban Kasa Buhari Ya Kara Jajircewa Wajen Kawo Sababbin Tsare-Tsare A Wa’adin Mulkin Sa Na Biyu,Musamman Magance Af’kuwar Miyagun Ayyuka A Lokacin Gudanar Da Zabe Domin Tabbatar Da Martabar Nijeriya A Idon Duniya

Leave a Reply