Home Labaru Kiwon Lafiya Tsaro: Wani Jirgin Yakin Nijeriya Ya Tarwatsa Maboyar ‘Yan Boko Haram A...

Tsaro: Wani Jirgin Yakin Nijeriya Ya Tarwatsa Maboyar ‘Yan Boko Haram A Sambisa

416
0

Dakarun Sojin Saman Operation LAFIYA DOLE Sun Kai Mumunan Hari Kan Yan Tada Kayar Bayan Boko Haram A Unguwar Alafa Dake Cikin Dajin Sambisa, Jihar Borno A Ranar Litinin, 10 Ga Watan Yuni, 2019.
Kakakin Hukumar Sojin Saman, Bimbo Daramola, Ya Bayyana Wannan Ne A Wani Jawabin Da Ya Saki Da Yammacin Yau Litinin, Yace: “Dakarun Sojin Sama Na Rundunar Operation Lafiya Dole Sun Samu Wani Nasara Kan Yan Ta’addan Boko Haram Dake Zaune A Dajin Sambisan Jihar Borno.”
“Harin Wanda Ya Kai Ga Ragargaza Babbar Cibiyar Taronsu Tare Da Hallaka Yan Ta’adda Da Dama, Ya Gudana Ne A Yau 10 Ga Yuni 2019, Bayan Bincikin Na’ura Ya Gano Wata Rumfa A Alafa Cikin Dajin Sambisa Inda Yan Ta’addan Ke Amfani Da Shi Wajen Baiwa Maharansu Umurni.”
Yayinda Jirgin Ya Gano Gidan Daga Sama, Ya Hangoshi Cike Da Yan Ta’addan A Cikin. Ba Tare Da Bata Lokaci Ya Sakar Musu Wutar Aradu Wanda Ya Ragargaza Cibiyar Tare Da Kisan Yan Ta’addan.”

Leave a Reply