Fararen hula da dama sun tsere daga gidajen su sakamakon wani hari da ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne, suka kai a garin Gubio dake arewacin jihar Borno.
Karanta Wannan: Arewa Maso Gabas: Sojoji Sun Yi Maganin Wasu ‘Yan Boko Haram A Garin Kollarum
Maharan dai sun dira garin wanda shi ne shelkwatan karamar hukumar Gubio ne a misalin karfe 5:40 na yamma, yayin da suka fara harbin kan mai-uwa da wabi, wanda hakan ya tilastawa mazaunan yankin gudu zuwa daji.
Wata majiya daga kungiyar sa kai, ta ce maharan sun matsa zuwa garin Mugumeri da misalin karfe 9:00 na dare, inda suka kashe mutane da dama, kuma suka barnatar da kayayyaki na miliyoyin nairori.
Sun kara da cewa sun kona gidaje da dama, kuma sun kona dukkan kayayyakin hanyar sadarwa, sannan kuma sun kashe mutane da dama, wanda yanzu haka ba a san adadin rayuka da dukiyoyin da aka rasa ba.
You must log in to post a comment.