Home Labaru Rikicin Kashmir: An Cigaba Da Musayar Wuta A Tsakanin Indiya Da Pakistan

Rikicin Kashmir: An Cigaba Da Musayar Wuta A Tsakanin Indiya Da Pakistan

480
0

Akalla mutane biyu sun mutu ciki har da wani jami’in dan sanda da kuma wani da ake kyautata zaton dan ta’adda ne yayin wata musayar wuta da safiyar Laraban nan a yankin Kashmir, sa’o’i kalilan bayan Donald Trump, na Amurka ya sha alwashin shiga tsakani don magance rikicin da ya kunno kai tsakanin Indiya da Pakistan.

Rikicin dai shi ne karon farko da aka fuskanta tun bayan da Indiya ta kwace ikon yankin na Kashmir mai rinjayen musulmi, wanda kasashen biyu suka juma suna takaddama akan sa.

A bangare guda Pakisatn ta fitar da sanarwar da ke nuna cewa jami’an tsaron Indiya sun hallaka mata mutane akan iyakar yankunan biyu ta hanyar harbin bindiga tun daga nesa.

Sai dai makamancin labarin da wata Jaridar Indiya ta wallafa ya nuna cewa, dan sandan Indiya 1 ya mutu yayinda wasu fararen hula 4 kuma suka jikkata bayan da jami’an tsaron Pakistan suka bude musu wuta akan iyakar kasashen biyu.

Kasashen Indiya da Pakistan, masu karfin makamin Nukiliya, rikicin su kan yankin na Kashmir tun bayan rabuwar su a shekarar 1947 babbar barazana ce ga tsaron nahiyar ta Asiya, a dai dai lokacin da a bangare guda itama Sin wato China ke ikirarin mallakar wani bangare daga yankin da su ke rigima akai.