Home Labarai Ta’addanci: An Sace Yara 4 ’Yan Gida Ɗaya A Kaduna

Ta’addanci: An Sace Yara 4 ’Yan Gida Ɗaya A Kaduna

29
0
114495633 gunmen
114495633 gunmen

Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun sace wasu ƙananan yara 3 ’yan gida daya a yankin New Millennium City da ke Ƙaramar Hukumar Chikun a Jihar Kaduna.

A cikin daren ranar Talata ne maharan suka kutsa gidan suka yi awon gaba da yaran  mata uku suka bar ƙanin su namiji, mai shekara biyu a duniya.

An sace yaran ne yayin da mahaifun su ya je asibiti domin duba mahaifiyar su, bayan an kwantar da tagwayen da ta haifa a kwanakin baya.

Mahaifin yaran, Injiniya Yunusa Adamu, Sarkin Matasa, ya shaida cewa, ƙanin yaran da ke barci ya tsallake rijiya da baya, maharan ba su gan shi ba.

Injiniya Yunusa, ya ce, da daddare abin ya faru, bayan ya dawo yana shigowa sai ya samu gidan a buɗe, sun tafi da yaran, dayan da ke barci ya lulluɓe jikin sa ne kawai aka bari, ba su gan shi ba, Allah ya kiyaye shi.

Ya shaida cewa, har yanzu babu wanda ya tuntuɓe su a kan lamarin.

Leave a Reply