Robert Lewandowski ya zama dan wasa na uku da ya zura kwallaye 100 a gasar cin kofin zakarun Turai yayin da Barcelona ta lallasa Stade Brestois da 3 da 0 a wasan da suka fafata ranar Talata.
Cristiano Ronaldo ne kawai mai kwallo 141 da Lionel Messi mai 129 suka fi ɗan wasan mai shekara 36 a yawan kwallaye na gasar zakarun Turai.
Lewandowski ya zura kwallon sa ta 100 a minti na 10 da fara wasa, kuma shine ya ci kwallye biyu cikin ukun da ƙungiyar ta yi nasara.
Dani Olmo kuwa ya ci wa Barcelona kwallon sa ta farko a gasar cin kofin zakarun Turan.
Barcelona ta koma matsayi na biyu a teburin gasar da maki 12, bayan ta yi nasara a wasanni hudu cikin biyar, yayin da Brest ta koma matsayi na tara.