Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya gana da wakilan shugabannin kungiyoyin ‘yan Nijeriya mazauna kasar Japan, yayin halartar taron kasa da kasa a kan ci-gaban kasashen nahiyar Afrika karo na bakwai da ke gudana a birnin Yokohama.
Buhari ya bayyana cewa, ya amince da cewar akwai wasu ‘yan Nijeriya da ke aikata miyagun laifuffuka a kasashen ketare,yana mai cewa irin wadannan batagarin ba wakilan kasa nagari neba.
Kalaman shugaba Buhari dai su na zuwa ne, a daidai lokacin da gwamnatin kasar Amurka ta kama wasu ‘yan Nijeriya 80 da laifuffukan zamba da damafara.
Shugaba Buhari, ya jaddada aniyar gwamnatinsa na yaki da aikata miyagun laifuffuka a gida da waje, yayin da ya bukaci ‘yan Nijeriya mazauna kasar Japan su zama jakadun kasa nagari tare da yin biyayya ga dokokin kasar da suke zaune.














































