Home Labaru Karin Haske: CBN Ya Ce Bai Hana Karbar Tsoffin Kudi A Najeriya...

Karin Haske: CBN Ya Ce Bai Hana Karbar Tsoffin Kudi A Najeriya Ba

953
0
Babban bankin Nijeriya
Babban bankin Nijeriya

Babban Bankin Najeriya wato CBN ya karyata rade-radin da ake yadawa cewa ya hana  karbar tsoffin kudi a Najeriya,  inda ya ce ya hana bankuna ba jama’a tsoffin kudade ne kawai.

Wasu ‘yan Najeriya suka shiga rudani dangane da wata jita-jitar dake cewa za a daina karbar tsofaffin takardun kudi a bankunan najeriya nan da zuwa wani lokaci, sai dai wani babban jami’i a daya daga cikin manyan bankunan ya ce mutane basu fahimci sanarwar bace.

Daya daga babban darakta a bankunan kasuwanci Mallam Haruna Musa, ya ce  a umurnin da CBN ya ba su babu inda aka ce su sanya wani wa’adi na daina karbar tsohon kudi.

Rahotanni sun nuna cewa jita-jitar ta sa wasu na karyar da darajar kudadensu, wadanda suke ganin sun tsufa, inda wasu kan bayar da naira dubu daya a ba su naira dari bakwai.

Jami’in ya ce CBN ne ya zo da tsari domin kyautata yanayin takardun kudin da jama’a ke amfani da su kasancewar karuwar jama’ar da kasar ke da su, da suka kai kimanin miliyan dari biyu.

A don haka ne ya ce babban bakin ya bayar da umarni ga dukkanin bankunan kasar da idan za su ba wa mutane ko masu mu’amulla da su kudi, kada su sake ba su tsohon kudi.