Home Labaru Ta’addanci: An Kama Alburusai 10,000 A Hannunsu Wasu Yan Bindiga

Ta’addanci: An Kama Alburusai 10,000 A Hannunsu Wasu Yan Bindiga

351
0

 Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jahar Oyo ta kama wasu ‘yan bindiga guda hudu da suka shahara wajen safarar makamai da alburusai ga kungiyoyin ‘yan fashi da makami da masu garkuwa da mutane a jihar.

Karanta Wannan: Harin ‘Yan Bindiga: Al’ummomi Na Ci-Gaba Da Kaurace Wa Muhallansu A Jihar Katsina

Rundunar ta kama mutanen ne dauke da alburusai guda dubu 10, kamar yadda kwamishinan ‘yan sandan jihar, Shina Olukolu ya bayyana, inda ya ce sun  kama mutanen a unguwar Oke-Bola na garin Ibadan.

Kwamishinan ya ce ‘yan bindigan sun boye makaman ne a cikin wata mota kirar Toyota Sienna da Toyota Camry, guda daga cikinsu ya bayyana cewa ba su da lasisin siyar da harsashi, amma ya na kai wa mafarauta alburusai.

Kwamishinan ya kara da cewar za su ci gaba  gudanar bincike kan wadanda aka kama a jihar.