Rundunar sojin Najeriya ta Operation UDO KA ta ce an kashe jami’an ta guda biyu a wani shingen bincike a kan hanyar Umuahia- zuwa Owerri da ke jihar Abia.
Wata sanarwa da Laftanar Kanar Jonah Unukhalu na rundunar ya fitar, ya ce lamarin ya afku ne ranar Laraba, inda ya ce suna zargin ƴan awaren Biafra da kuma takwarorin su na ESN da kai harin.
Sanarwar da sojojin suka fitar ta ce dakarun sun samu nasarar daƙile harin da aka kai, abin ya sa wasu daga cikin maharan suka tsere da raunuka har da barin motocin su a wurin.
Sai dai ya ce abin takaici shi ne yayin artabu da waɗanda suka kai harin, sojojin Rundunar biyu sun mutu.
Wannan dai shi ne hari na biyu kan shingen binciken sojoji a jihar ta Abia, tun bayan wanda ya lakume rayukan sojoji biyar a watan Mayu.














































