Home Labarai Rashin Inganci: Gwamnan Edo Ya Umarci ‘Yan Kwangila Su Koma Bakin Aiki

Rashin Inganci: Gwamnan Edo Ya Umarci ‘Yan Kwangila Su Koma Bakin Aiki

204
0
Monday Okpebholo6
Monday Okpebholo6

Gwamna Monday Okpebholo na jihar Edo ya umurci ‘yan kwangila su koma wuraren aiki tare da gyara ayyukan su da suka lalace a babban birnin jihar wato Benin.

Okpebholo ya ba da wannan umarni ne a ziyarar gani da ido na titin ‘Upper Mission Extension Road’ da ke hanyar madatsar Aduwawa da ‘Ramat Park’ a Benin.

Okpebholo ya ce, gwamnatin sa bisa sabon tsarin shugaba Tinubu na ‘sabunta fata na gari’, ya dukufa wajen dawo da fata nagari ga mutanen Edo.

Da yake nuna rashin jin dadin sa game da halin da hanyoyin ke ciki, Okpebholo ya tabbatar wa jama’a cewa, za a fara aiki nan take, inda ya kara da cewa, a shirye ya ke ya mika romon dimokuradiyya ga jama’ar sa.

Ya jaddada cewa, al’ummar Edo sun cancanci hanyoyi masu kyau kuma masu rai.

Leave a Reply