Home Labaru Ta Kacame A Kan Bidiyon Da Ke Nuna A’isha Buhari Ta Na...

Ta Kacame A Kan Bidiyon Da Ke Nuna A’isha Buhari Ta Na Fada

716
0

Baraka ta kunno kai a Fadar Shugaban kasa da ke Abuja, a daidai lokacin da ake yada jita-jitar cewa Shugaba Muhammadu Buhari zai yi wa matar sa A’isha Buhari kishiya.

A ‘yan kwanakin nan dai, wani bidiyo ya rika yawo a shafukan sada zumunta, wanda a cikinsa aka ga uwargidan Shugaban kasa ta na ta fada da harshen Turanci ta na gaurayawa da Hausa.

Jama’a da dama a shafukan sada zumunta sun rika alakanta bidiyon da cewa, A’isha Buhari ce ta dawo daga Ingila ta na fada cewa an rufe mata kofa.

Yayin da kafar yada labarai ta BBC ta zanta da ita, A’isha Buhari ta tabbatar da cewa ita ce aka dauka a cikin bidiyon, amma ta ce tsohon bidiyo ne, ta na mai karin haske da cewa Fatima ‘yar gidan Mamman Daura ce ta dauki bidiyon da ake tafka mahawara a kai.

Sai dai bayan BBC ta tuntubi Fatima Mamman Daura ba ta musanta daukar bidiyon ba, amma ta ce ta dauki bidiyon ne domin ta nuna wa iyayen ta da jami’an tsaro a matsayin shaida ko da wani abu ka biyo baya.