Home Labaru Abubakar Shekau Ya Ce Ba Za Su Daina Kashe Mutane Ba

Abubakar Shekau Ya Ce Ba Za Su Daina Kashe Mutane Ba

566
0
Abubakar Shekau, Shugaban Kungiyar Boko Haram
Abubakar Shekau, Shugaban Kungiyar Boko Haram

Bayan likimon da ya yi na tsawon lokaci, Shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ya ya maida wa Gwamnan Jihar Borno Babagana Zulum kakkausan martani.

Shekau ya maida wa Gwamnan martani ne, bayan ya yi bayanin cewa ‘yan Boko Haram su ajiye makamai su mika wuya domin su samu shiga cikin Shirin Afuwar Gwamnatin Tarayya.

A cikin wani sakon mintuna 18 da aka rika yada muryar Shekau ya na magana a cikin harsunan Kanuri da Hausa ya karyata gwamna Zulum, wanda ya ce wasu mabiya Boko Haram da aka tilasta wa shiga ba da son ran su ba sun gaji da yakin da ake yi.

Shekau ya ce babu wani dan kungiyar su ko daya da ya gaji da yaki, kuma za su cigaba da yakin har lokacin da mutuwa za ta dauki ran su.

Wannan ne bidiyon farko da Shekau ya fitar tun bayan watanni masu yawa da aka daina jin labarin sa.

A tsakiyar bidiyon kuma, Shekau ya sanya muryar Gwamna Zulum, inda ya ke jawabi a gaban jama’a ya na kiran ‘yan Boko Haram su mika wuya domin su ci amfanin shirin afuwa na gwamnatin tarayya.