Home Addini Sulhuntawa: Daurawa Ya Shiga Ofis Bayan Dawowarsa Hisbah

Sulhuntawa: Daurawa Ya Shiga Ofis Bayan Dawowarsa Hisbah

308
0

Babban kwamandan hukumar Hisbah ta Jihar kano, Sheikh
Aminu Ibrahim Daurawa ya isa ofishinsa a karon farko bayan ya
dawo bakin aiki.


Karon farko ke nan da mashahurin malamin ya shiga harabar ofishin hukumar tun da ya sanar da murabus dinsa a ranar Juma’a kan sukar da Gwamna Abba Kabir ya yi wa salon kamen hukumar a aikinta na yaki da masu badala a jihar.


Ajiye aiki Daurawa ya bar baya da kura inda aka yi ta ba shi baki, gwamnatin jihar kuma ta shiga bikon sa.


A karshe ranar Litinin da dare aka shawo kansa a wani taron sirri da zauren Malaman Kano ya jagoranta a gidan gwamnatin jihar

Leave a Reply