An dauki nauyin karatun jami’ar matashin nan dake sana’ar
haya da babur din a Daidaita Sahu, wanda ya mayar da Naira
miliyan 15 da ya tsinta a babur dinsa.
Tsohon dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar LP a zaben 2023, Peter Obi da mataimakinsa, Datti Baba-Ahmed ne suka auki nauyin karatun matashi mai suna Auwal Salisu.
Peter Obi da Datti sun dauki nauyin Auwalu mai shekaru 22 har sai ya kammala karatu a Jami’ar Baze mai zaman kanta dake
Abuja, inda za su rika biya masa kudin makaranta da na abinci da na dakin kwana da sauran bukatu.
Auwalu mai shekaru 22 ya mayar da kudin da wani fasinjansa ya bari a cikin babur dinsa ne bayan da ya ji cigiyar kudin a gidan rediyo.