Home Labaru Sulhu: ‘Yan Bindigar Katsina Sun Gabatar Da Bukatun Su Kafin Su Ajiye...

Sulhu: ‘Yan Bindigar Katsina Sun Gabatar Da Bukatun Su Kafin Su Ajiye Makamai

680
0

Yan bindigar da su ka addabi al’ummomin jihar katsina, sun shimfida ka’idojin ajiye makaman su, inda su ka bukaci a saki mutanen su da ke tsare a gidajen yari, a kuma duba yadda jami’an tsaro da sarakunan gargajiya da alkalai ke karbe masu dabbobi.

Da su ke magana yayin tattaunawa tsakanin su da Gwamna Aminu Masari a kauyen Dankolo, sun ce mafi akasarin su sun shiga harkar fashi ne saboda kiyayyar da mutanen garin da jami’an tsaro da sarakunan gargajiya da kuma alkalai ke nuna masu.

Daya daga cikin ‘yan bindigar Idris Yayande, ya ce wasu daga cikin mutanen su da aka kama sun hada da Alhaji Baldu, da Alhaji Lawal da Ibrahim Nakutama, ya yin da shi kan sa ya ce an kama shi ba tare da sanin laifin da ya aikata ba, kuma an tsare shi tsawon watanni 15 kafin a sake shi.

A na shi jawabin, Gwamna Masari ya tabbatar da cewa, wasu ‘yan bindiga su na tsare sama da shekaru 10, ya na mai cewa babu ta yadda za a rika ajiye mutane tsawon sama da shekaru biyu ba tare da wata tuhuma ba.