Wasu fusatattun masu zanga-zanga sun cinna wa gidan sakataren gwamnatin jihar Katsina Mustapha Inuwa da sakatariyar jam’iyyar APC wuta a karamar hukumar Danmusa.
Wata majiya ta ce, matasan sun cinna wa gidan wuta ne a daren ranar Talatar da ta gabata, domin zanga-zanga a kan yawan hare-haren ‘yan bindiga a yankin, da kuma yadda aka ci zarafin wani dan kasuwa a hanyar sa ta zuwa kasuwa.
Bayanai sun nuna cewa, matasan sun yi zanga-zanga a fadar hakimin garin, wanda ya tsere a lokacin da ya hange su.
Babban sakataren gwamnatin jihar Katsina dai ya fito ne daga yankin, kuma shi ne jagoran shirin yafiya da aka kafa domin magance matsalolin tsaro da ke damun jihar Katsina.
Kakakin
rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina SP Gambo Isah ya tabatar da lamarin, inda
ya ce masu laifin sun kona gidan sakataren, da ofisoshin jam’iyyar APC biyu, ya
na mai cewa tuni an kama mutane 35 da ke da nasaba da lamarin.