Home Labaru Sufuri: Nijeriya Za Ta Fara Saida Tikitin Shiga Jirgin Kasa A Yanar...

Sufuri: Nijeriya Za Ta Fara Saida Tikitin Shiga Jirgin Kasa A Yanar Gizo – ICRC

337
0

Yanzu haka shirye shirye sun yi nisa, na fara saida tikitin shiga jirgin kasa daga Kaduna zuwa Abuja a shafukan yanar gizo, domin kauce wa badakalar da ake samu a tashoshin jirgin, wanda ya ke janyo rikici tsakanin matafiya da jami’an hukumar.

Chidi Izuwah, Shugaban Hukumar Ta ICRC
Chidi Izuwah, Shugaban Hukumar Ta

Hukumar da hakkin tsara cinikin yanar gizo a Nijeriya ya rataya a wuya ta ICRC ta bayyana haka, yayin da shugaban ta Chidi Izuwah ya ke mika takardun kasuwancin ga ministan sufuri Rotimi Amaechi.

Chidi Izuwah ya bayyana wa Ameachi cewa, kamar yadda ya yi alkawarin samar da mafita ga yamutsin da ake samu a tashoshin jiragen kasa, shi ya sa su ka kai ma shi cikakkun bayanan kasuwancin sayen tikiti ta yanar gizo.

A karshe minista Amaechi ya bayyana farin cikin sa da wannan takarda, tare da gode wa shugaban hukumar bisa kokarin da ya yi wajen kammala wannan aiki a cikin kankanin lokaci, ya na mai tabbatar ma shi cewa zai mika lamarin ga majalisar zartarwa domin samun amincewa.