An gargadi shugabannin kungiyar kiristoci ta CAN su gujewa shiga harkokin siyasa a Najeriya.
Shugaban kungiyar fastocin arewa John Abu Richard, ya bayanna haka a lokacin da yake magana akan irin sharhi da wasu shagabannin kungiyar CAN ke yi akan gwamnatin shugaba Buhari.
Abu Richard, ya bukaci shugabannin kungiyar su ba shugaban kasa Muhammadu Buhari hakuri akan furucinsu,ya ce kalaman na shugabannin CAN ba su da ce da gwamnatin Buhari ba.
Ya ce shugabannin CAN na shiga manyan lamuran tsaro wanda ka iya sanya Najeriya cikin matsanancin rikici, inda ya kara da cewa a matsayinsu na malamai, littafi mai tsarki ya umurce su da mu yi wa shugabanninmu addu’a ba tare da la’akari da kabila ko addini ba.
Ya ce abinda takaicin a yanzun shi ne alkiblar kungiyar CAN ita ce kokarin ba ta gwamnatin shugaba Buhari da kuma juya zukatan yan Najeriya akan gwamnati.
You must log in to post a comment.