Home Labaru Ruga: Jahohi Ya Kamata Su Fara Shirin-Gwamna Ganduje

Ruga: Jahohi Ya Kamata Su Fara Shirin-Gwamna Ganduje

215
0

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya koka a game da irin abinda mutanen Najeriya ke yi wa alummar Fulani makiyaya.

Ganduje, ya yi magana akan shirin RUGA da a ke so a kawo wasu jahohin Najeriya, ya cewa bai kamata a kawo shirin RUGA a jihohin da ba na Fulani ba.

Abdullahi Umar Ganduje, Gwamnan Jihar Kano

Gwamnan ya bayanna hakan ne a lokacin da ya zantawa da manema labarai a jihar Sokoto bayan kamala wani daurin aure,inda ya ce  ya na son tsarin RUGA da aka dakatar ya zama na ganindama ba wai tilas ba, kuma  kamata ya yi a bar wa jihohi damar dabbaka shirin RUGA.

Gwamnan jihar Kano, ya ce asali ma gwamnatin jihohi ne ya kamata a ce sun zo da tsarin gina RUGA domin habakar tattalin arzikin Makiyaya Fulani ba gwamnatin tarayya ba.