Home Labaru Sulhu: Shugaba Buhari Zai Tafi Ƙasar Mali

Sulhu: Shugaba Buhari Zai Tafi Ƙasar Mali

413
0

A yau Alhamis ne Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai tafi kasar Mali domin shiga tsakani a rikicin kasar.

SHUGABA BUHARI DA GOODLUCK JONATHAN

Tafiyar ta shugaban ƙasar ta biyo bayan tattaunawarsa da Tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan, wanda yana daga cikin masu shiga tsakani daga ƙunigyar Ecowas da suka je Mali domin kawo sasanci akan rikicin.

Wasu daga cikin shugabannin ƙasashen Yammacin Afrika irin su Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou sun amince su hadu a Mali domin tattaunawa don kawo sasanci tsakanin Shugaban Mali Boubakar Keita da kuma ‘yan adawa a ƙasar.

Ana sa ran Shugaban Ghana Nana Akufo Addo da kuma na Cote d’Ivoire Alassane Ouattara za su halarci tattaunawar.

A zantawarsa da manema labarai mai Magana da yawun shugaban kasa Malam Garba Shehu yace Shugabannin na Ecowas za su tattauna ne da bangarorin Mali bayan tawagar tsohon shugaban kas Goodluck Jonathan sun kasa gano bakin zaren warware rikicin.

Wannan ne karo na farko da Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai fita Najeriya tun bayan da aka rufe iyakokin ƙasar nan sakamakon annobar cutar korona.

Leave a Reply